Sarkin Birtaniya, Charles na III ya shirya liyafar cin abinci ta musamman a Fadar Windsor a ranar Talata domin karrama Sarkin Oman, Sultan Haitham bin Tarik.
A yayin liyafar, ya yaba da ƙoƙarin Oman na samar da zaman lafiya, tare da ambaton wani hadisi na Annabi Muhammad (SAW) cikin harshen Larabci.
Wannan ba shi ne karon farko da Sarki Charles ya yi magana da Larabci a wani taron hukuma ba.
A watan Disamban 2024, ya yi maraba da Sarkin Qatar a Fadar Buckingham da harshen Larabci. A shekarar 2013 kuma, an bayyana cewa Charles ya fara koyon harshen Larabci tun yana Yarima.
