Gamayyar jam’iyyun Larabawan Isra’ila ta Joint List ta bayyana goyon bayanta ga jagoran ’yan adawa, Gadi Eisenkot, domin ya kafa sabuwar gwamnati bayan zaɓen ƙasar da aka gudanar a ranar 27 ga Oktoba.
Matakin ya sa Eisenkot samun goyon bayan ‘yan majalisa 67 daga cikin 120 na Majalisar Dokokin Isra’ila, wato Knesset, inda ake buƙatar aƙalla kujeru 61 domin samun rinjaye.
Jam’iyyun Larabawan Isra’ila sun lashe kujeru 19, ciki har da 11 na Joint List da takwas na Ra’am, yayin da gamayyar Firaminista Benjamin Netanyahu ta samu kujeru 53.
Sai dai goyon bayan da Eisenkot ya samu ba ya nufin cewa ya riga ya kafa gwamnati, domin har yanzu ana buƙatar cimma yarjejeniya tsakanin jam’iyyun.
Shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, ya ce zai yanke shawarar wanda zai bai wa damar fara kafa sabuwar gwamnati a ranar Lahadi, 8 ga Nuwamba.
