Wata ‘yar siyasar Amurka kuma mai harkokin hulɗa da jama’a, Diana London, ta musanta zargin karɓar dala miliyan 4.5 daga gwamnatin Shugaba Bola Tinubu domin inganta martabar Najeriya a Amurka.
London ta bayyana cewa ziyarar da ta kai Najeriya ta kasance ne domin gudanar da wata hira ta musamman da Shugaba Tinubu.
Ta bayyana a shafinta na X tana mai cewa zargin karɓar kuɗin yunƙuri ne na ɓata mata suna, tana mai cewa babu gwamnatin Najeriya ko wani mutum a kasar da ya biya ta wannan makudan kudade.
Sai dai jaridar TheCable ta ruwaito cewa takardun da aka gabatar ƙarƙashin dokar rajistar wakilan ƙasashen waje ta Amurka FARA sun nuna cewa kamfanin London ya karɓi jimillar dala 662,000 daga DCI Group, wanda ke gudanar da ayyukan hulɗa da jami’an Amurka a madadin gwamnatin Najeriya.
Rahoton ya bayyana cewa dala miliyan 4.5 wani ɓangare ne na yarjejeniyar gwamnatin Najeriya da DCI Group.
A nasa ɓangaren, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya buƙaci fadar shugaban ƙasa ta bayyana cikakkun bayanai kan yarjejeniyar da kuɗaɗen da aka kashe.
