Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da muƙaddashin babban sakataren ƙungiyar, Benson Upah, ya sanya wa hannu a Abuja ranar Alhamis, bayan wani taro tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago ya tashi ba tare da cimma matsaya ba.
NLC ta bayyana cewa rashin cimma matsaya a tattaunawar ya sa ta sake jaddada buƙatar gwamnati ta ɗauki matakan da suka dace domin magance matsalolin ma’aikata.
Ƙungiyar ta kuma yi gargaɗin cewa idan gwamnati ta kasa cika buƙatun ma’aikata kafin wa’adin da ta bayar, za ta iya ɗaukar matakan ƙwadago a faɗin ƙasar.
