Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta zargi rundunar ’yan sandan Najeriya da amfani da kotuna a matsayin hanyar matsa lamba da takura wa ’yar jarida Farida Isiak.
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda ake amfani da kotuna wajen musgunawa ’yan jarida, lamarin da take ganin zai iya kawo cikas ga ’yancin faɗar albarkacin baki da kuma aikin jarida a ƙasar.
Amnesty International ta jaddada muhimmancin kare ’yan jarida daga duk wani nau’in tsoratarwa ko matakin da zai hana su gudanar da ayyukansu cikin ’yanci da bin ƙa’idojin aikin jarida.
Haka kuma, ƙungiyar ta yi kira da a mutunta haƙƙoƙin ’yan jarida da kuma tabbatar da cewa duk wani matakin shari’a da ake ɗauka a kansu ya kasance bisa doka da kuma bin ƙa’idojin adalci.
