Wata Babbar Kotun Shari’a a jihar Kano ta umarci rundunar ’yan sanda da ta gudanar da bincike kan zarge-zargen haɗa baki wajen aikata laifi, cin zarafi, tsoratarwa da kuma rushe dukiya ba bisa ƙa’ida ba da ake yi wa Muazu Abdullahi-Gwarzo, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazaɓar Gwarzo/Kabo a majalisar tarayya.
Umarnin kotun ya biyo bayan ƙorafin da wani mazaunin ƙaramar hukumar Gwarzo, Sulaiman Isah, ya shigar, inda ya zargi ɗan majalisar, wanda aka fi sani da Baban Gandu, da rushe masa gini, cin zarafinsa da kuma yi masa barazanar kisa kan batun sayen wata dukiya.
Mai ƙorafin ya yi zargin cewa rikicin ya samo asali ne daga sayen kadarar da ya yi, lamarin da ya haifar da takaddama tsakaninsa da ɗan majalisar.
Kotun ta umarci ’yan sanda da su binciki zarge-zargen domin gano gaskiyar lamarin da kuma ɗaukar matakan da suka dace bisa doka.
