Saurari premier Radio
31 C
Kano
Monday, April 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRundunar Yan sandan Kano ta shawarci jami'iyyun NNPP,APC da PDP da su...

Rundunar Yan sandan Kano ta shawarci jami’iyyun NNPP,APC da PDP da su dage taron yakin neman zabensu na wannan ranar

Date:

Rundunar yan sandan jahar Kano , ta shawarci jam’iyyun siyasa a jihar, da su dage yakin neman zabensu na dan takarar shugaban kasa da na yan majalissun tarayya har zuwa bayan zaben shugaban kasa.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya rabawa labarai a birnin Kano.

Sanarwar ta ce jam’iyun siyasar sun hada APC,NNPP da kuma PDP wadanda suka sanar da rundunar yan sandan jahar Kano za su gudanar da yakin neman zaben su a ranar Alhamis 23 ga watan Fabarairu 2023.

Rundunar ta kara cewa kasancewar jam’iyun za su gudanar da yakin neman zaben a kusa da juna , wanda hakan zai iya haifar da matsalar rashin tsaro , ta shawarce su da daga zuwa nan gaba dan samun zaman lafiyar Kano.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammad Yakubu ya gayyaci dukkanin jam’iyun domin tattauwa da su kan lamarin wanda har aka kammala zaman ba a samu matsaya ba.

Kakakim rundunar yan sandan Kano SP ya ce kwamishinan ya roke su da su duba zaman lafiyar da ake da shi a jihar Kano su janye.

Latest stories

Related stories