Saurari premier Radio
40.8 C
Kano
Friday, March 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiZaben 2023: Shugaba Buhari ya kawo akwatinsa | Premier Radio | 26.02.2023

Zaben 2023: Shugaba Buhari ya kawo akwatinsa | Premier Radio | 26.02.2023

Date:

Jam’iyyar APC ta lashe akwatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, da kuri’u 523 a mazabar Sarkin Yara A dake garin daura  jihar Katsina.

Har ila yau, PDP ta sami kuri’u 3, yayinda jam’iyyun NNPP da LP basu sami ko kuri’a 1 ba.

Buhari ya kada kuri’arsa ce tare da mai dakinsa, Hajiya Aisha Buhari, da sauran iyalai a akwati guda.

Jim kadan bayan kada kuri’ar tasa ce ya shaidawa yan jarida yakinin da yake da shi cewa jam’iyyar sa ce zata lashe zaben shugaban kasa, daga Daura zuwa Lagos.

A yau Lahadi, za’a cigaba da kada kuri’a a wasu mazabu dake sassan kasa Najeriya, biyo bayan matsalolin da aka samu masu alaka da na’urar tantancewa ta BVAS.

Latest stories

Related stories