41.7 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
HomeLabaraiYan Sanda Dubu 18 Ne Zasu Sanya Ido a Harkokin Zabe a...

Yan Sanda Dubu 18 Ne Zasu Sanya Ido a Harkokin Zabe a Jihar Kano.

Date:

Rundunar yan sandan jihar Kano tace ta tura jamiā€™ai sama da dubu 18 domin sa’ido da kuma tabbatar da an gudanar da zaben kasar nan lafiya.

Kwamishinan yan sandan Kano, CP Mamman Dauda ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a shalkwatar rundunar da ke Bompai a Kano.

Yace a kokarinsu na ganin an yi zabe a tsaftace kuma cikin kwanciyar hankali, rundunar ta kama mutane 365 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a Kano cikin makonni bakwai da suka gabata.

Ya kara da cewa a lokuta da dama, rundunar ta kama tare da gurfanar da yan siyasa da laifuka daban-daban.

Latest stories

Related stories