31.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
HomeLabaraiGwamnatin tarayya zata biya ma'aikatan Npower dake binta bashi hakkokinsu.

Gwamnatin tarayya zata biya ma’aikatan Npower dake binta bashi hakkokinsu.

Date:

Ma’aikatar jin ki da kare afkuwar bala’ai ta ce nan ba da dadewa ba za ta biya ma’aikatan rukunin C na shirin Npower hakkokinsu.

Ma’aikatar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun ministar maaikatar, Sadiya Umar Farouk da shafin Npower ya wallafa a kafar Facebook.

Sanarwar ta ce a cikin wannan mako za a biya ma’aikatan na Npower alawus-alawus dinsu na Oktoba, Nuwamba da Disamba, 2022.

A cewar sanarwar, an samu tsaiko wajen biyan alawus-alawus din ne sakamakon wasu matsaloli da suka shafi tangardar na’ura da kuma karkare shekarar kudi ta 2022.

Tun a Oktoba, 2022 ne ma’aikatan Npower na Rukunin CII suka fara ayyuka a wurare daban-daban, amma ba a taba ba su alawus ba.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...