Saurari premier Radio
35.7 C
Kano
Sunday, April 28, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiNNPC ya ci gaba da hako man fetur a Borno, bayan dakatar...

NNPC ya ci gaba da hako man fetur a Borno, bayan dakatar da aikin na shekaru 6

Date:

Kamfanin man fetur na Najeriya NNPC ya ci gaba da aikin hako mai a tafkin Chadi da ke jihar Borno, shekaru shida bayan dakatar da aikin.

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai halarci bikin ta allon gani gaka, tare da kaddamar da aikin hakar rijiyar mai na Wadi-B a yankin Tuba, karamar hukumar Jere.

A cewar jami’an Hukumar Kula da Makamashi ta NNPC, ana gudanar da aikin ne a karkashin hukumar binciken man fetur ta kasa NNPC na Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya, NUPRC.

Rahotonni sun bayyana cewa, an fara binciken man fetur a yankin tun a shekarar 1976.

Da yake bayyana yadda ake gudanar da aikin, babban daraktan hukumar kula da ayyukan hakar mai a kamfanin NNPC, Mukhtar Zanna, ya ce kamfanin na NNPC zai ringa tona kafa 14,000 a cikin rijiyar Wadi-B domin samun mai da iskar gas.

 

Latest stories

Related stories