Saurari premier Radio
40.8 C
Kano
Friday, March 29, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar Gwamnonin kasar nan ta samu sabon shugaba

Kungiyar Gwamnonin kasar nan ta samu sabon shugaba

Date:

Shugaban kungiyar gwamnonin kasar nan Aminu Tambuwal Ya ce sun dakatar da yankar kudade daga asusun jihohi kan bashin kudin London da Paris Club.

Aminu Tambuwal wanda kuma shi ne gwamnan jihar Sokoto ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa takwarorinsa bayani a ganawar da suka a ranar Talata a Abuja.

Ya ce ministar kudi ta yi alkawarin tabbatar da ganin an mayar wa da jihohin kudin da aka yanke a baya.

Ana dai ganin batun yankar kudin Paris Club ya kasance babban abin takaddama tsakanin gwamnatin tarayyar da gwamnatin jihohi a baya-bayan nan.

Haka ma dai kungiyar ta bayyana an samu shugabanci a kungiyar inda mambobin suka amince da sasanto gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq ya zama sabon shugaba, yayin da Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya zama mataimaki.

Latest stories

Related stories