Farfesa na farko a fannin ilmin kasa a Afirka, Jamiu Mosobalaje Oyawoye, ya rasu a yammacin ranar Litinin da ta gabata yana da shekaru 95.
Marigayin ya rasu ne sakamakon rashin dake da alaka da tsufa, a gidansa da ke karamar hukumar Offa a jihar Kwara.
Za a yi jana’izarsa da karfe 4 na yammacin yau, kamar yadda wakilinmu ya tattaro a daren Litinin.
Marigayi Baba Adini na jihar Kwara ya bar mata biyu da ‘ya’ya 10, inda za a yi jana’izarsa da karfe 4 na yammacin talatar nan.
Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi na kasa.
An haife shi a garin Offa a jihar Kwara a ranar 12 ga watan Agusta 1927, ya yi koyarwa a jami’ar Ibadan tsakanin 1960 zuwa 1977.
An nada shi Farfesa a shekarar 1966 yana da shekaru 39 kuma ya zama na farko Farfesa a fannin ilimin kasa a Afirka.