Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiShugaban Amurka ba zai halarci rantsar da Tinubu ba, ya turo wakilai

Shugaban Amurka ba zai halarci rantsar da Tinubu ba, ya turo wakilai

Date:

Shugaban kasar Amurka, Joe Biden ya sanar da tawagar da za ta  wakilce shi a wajen bikin rantsar da zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a ranar 29 ga Mayu, 2023, a Abuja.

Sanarwar da fadar White House ta fitar a yammacin jiya Litinin, ta ce sakatariyar ma’aikatar gidaje da raya birane ta Amurka, Marcia L. Fudge, ce za ta jagoranci tawagar.

Sauran ‘yan tawagar sun hada da jami’an Ofishin Jakadancin Amurka na Abuja Mista David Greene, Chargé d’Affaires.

Sai Marisa Lago, Mataimakiyar Sakatariyar Kasuwancin Kasa da Kasa a Ma’aikatar Kasuwancin Amurka.

Sanarwar ta kara da cewa Kwamandan Rundunar Sojojin Amurka mai lura da Afirka Janar Michael E. Langle shi ne zai wakilci rundunar sojojin Amurka a wajen taron, tare da Mary Catherine Phee, mataimakiyar sakatariyar harkokin wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya, bayan ya lashe zaben shugaban kasar, wanda aka gudanar a watan Faburairun da ya gabata.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories