Malamai a Abuja sun shiga zanga-zangar lumana tare da takwarorinsu a sassan Najeriya domin nuna rashin jin daɗinsu kan ci gaba da kai hare-hare kan makarantu da cibiyoyin ilimi a Najeriya.
Ƙungiyar malaman ta NUT ce ta jagoranci zanga-zangar, inda mahalarta suka riƙe alluna masu ɗauke da saƙonni daban-daban da ke kira ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa.
Masu zanga-zangar sun bi wasu manyan tituna da wurare a Abuja suna rera waƙoƙin haɗin kai tare da neman a sako malamai da ɗaliban da aka sace a jihohin Oyo da Borno a makonnin baya.
Da yake zantawa da manema labarai, shugaban NUT na ƙasa, Titus Amba, tare da Sakatare Janar na ƙungiyar, Clinton J. Ikpitibo, sun ce zanga-zangar ta zama dole domin isar da saƙon rashin gamsuwar malamai ga gwamnati.
Shugabannin ƙungiyar sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan makarantu, tare da yin garkuwa da malamai da ɗalibai, lamarin da suka ce na barazana ga ci gaban ilimi da tsaron makarantu a Najeriya.
Sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen kare makarantu da kuma tabbatar da ceto waɗanda aka sace cikin gaggawa.
