Rundunar Tsaro ta Civil Defence reshen Jihar Kano ta sallami wasu jami’anta na sa-kai guda biyar daga aiki bisa zargin aikata laifukan rashin ɗa’a da kuma saɓa wa ƙa’idoji da dokokin rundunar.
A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar a jihar, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar ranar Talata, ya ce kwamandan rundunar na Jihar Kano, Mohammed Hassan-Agalama, ne ya amince da korar jami’an bayan an same su da aikata abubuwan da suka saɓa wa ɗabi’u, ƙa’idoji da kuma tsarin aikin rundunar.
Sanarwar ta bayyana sunayen waɗanda aka sallama da suka haɗa da Yakubu Mubarak, Isma’il Muhd, Adamu Auwalu, Abdulrazaq Suleiman da Ahmad Sarki.
Ta ce rundunar ta kwace dukkan kayan aiki, kayan sawa na hukuma, katunan shaida da sauran kayayyakin da aka ba su a lokacin da suke aiki.
Kwamandan rundunar ya kuma umarci dukkan kwamandojin yankuna, jami’an ofisoshin shiyya da sauran jami’an da abin ya shafa a faɗin jihar da su ɗauki wannan mataki da muhimmanci, tare da tabbatar da cewa ba a sake ɗaukar waɗannan mutane a matsayin jami’an rundunar ba ko ba su wani aiki a madadinta.
Hassan-Agalama ya sake jaddada cewa rundunar ba za ta lamunci rashin ɗa’a ba, yana mai gargaɗin cewa duk wani jami’in da aka samu da aikata abin da zai bata sunan rundunar zai fuskanci hukuncin da ya dace.
Ya kuma tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tabbatar da ƙwarewa, gaskiya da kuma ingantaccen gudanar da ayyukanta kamar yadda doka ta tanada.
