Hukumar REMASAB ta musanta rahoton da wata kafar yada labarai ta wallafa, wanda a cikinsa aka yi ikirarin cewa ba’a biya ma’aikatan hukumar albashin su ba, kuma naira dubu10 kacal ake biyan ma’aikatan a kowane wata.
Wannan na kunshe ne cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Abubakar Ahmad ya fitar, inda sanarwar tace labarin bashi da alaƙa da ainihin halin da ake ciki a hukumar ta Remasab.
Da yake yiwa Premier radio krin bayani, jami’in yada labaran ya ce, a sanin hukumar babu wani ma’aikacinta da ake bawa albashin dubu 10, tare da nuna damuwarta kan yadda kafar ta yada mai cike da zarge-zarge ba tare da neman ƙarin bayani daga gare ta ba domin samar da adalci.
Hukumar ta kuma yi kira ga kafar da ta wallafa rahoton da ta gabatar da hujjojin da ta dogara da su wajen yaɗa labarin mai cike da zarge-zarge ko kuma su kuma su janye rahoton tare da fito da bayanan gaskiya.
Hukumar ta kuma sha alwashin ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da biyan albashin maaikatanta duk Wata, ba tare da bata lokaci ba, inda tace kawo yanzu ta biya duk bashin da ta gada a baya.
