Ƙungiyar wakilan kafafen yaɗa labarai ta Najeriya (Nigeria Correspondent chapel) reshen Kano ta bayyana cewa mambobinta sun amfana da tallafi da shirye-shiryen jin ƙai daban-daban a cikin shekara guda da ta gabata, yayin da shugabancin ƙungiyar ya gabatar da rahoton ayyukansa na shekarar da ta gabata.
Shugaban ƙungiyar, Murtala Adewale, ne ya bayyana hakan a wajen taron bikin cika shekara ɗaya na shugabancinsa da aka gudanar a Sakatariyar Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) da ke Kano.
Rahoton ya nuna cewa shugabancin ya bayar da tallafin jin ƙai na naira dubu dari biyar ga mambobi goma, ya taimaka wajen samar da rancen naira miliyan takwas da dubu ɗari biyar, ya kuma samar da guraben aikin Hajji guda biyu, tare da tallafawa da naira miliyan biyu domin kula da lafiyar Mamban su, sai kuma rabon kayan abinci na watan Ramadan da suka kai naira miliyan biyu da dubu ɗari biyar.
Da yake yiwa Premier radio karin bayani, Mataimakin Shugaban Ƙungiyar Yusuf Bala Nayaya ya ce shugabancin ya kuma samar da ƙarin tallafin naira dubu talatin a kowane wata ga mambobin ta, tare da ƙaddamar da shirye-shiryen bunƙasa ƙwarewar aikin jarida, ciki har da horaswa, kafa ƙungiyar haɗin gwiwa da kuma ba da lambobin yabo ga fitattun ‘yan jarida.
Da yake jawabi a wajen taron, Mai magana da yawun gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa wanda babban sakataren yaɗa labaran gwamnan Mustapha Muhammad ya wakilta ya jinjinawa ƙoƙarin mambobin ƙungiyar a fannin yaɗa labaran da suke yi cikin adalci tare da tallafa musu da naira miliyan 1 domin inganta ayyukan su.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito Shugaban ƙungiyar Murtala Adewale na cewa nasarorin ƙungiyar sun samu sakamakon haɗin kai da goyon bayan mambobin ta, yana mai jaddada cewa shugabancinsa zai ci gaba da aiwatar da shirye-shiryen inganta jin daɗin mambobi, ƙarfafa aikin jarida da bunƙasa ƙwarewar ‘yan jarida domin sauke nauyin da ya rataya a wuyansu yadda ya kamata.
