Mai Martaba Sarkin Karaye, Alhaji Muhammad Maharaz, ya aike da sakon taya murna ga Mataimakin Gwamnan Kano Alhaji Murtala Sule Garo, bisa nada shi a matsayin Mataimakin Gwamnan jihar.
Sarkin wanda a yanzu yana kasa mai tsarki, ya isar da sakon ne ta hannun wata tawaga daga Masarautar Karaye karkashin jagorancin Wamban masarautar Alhaji Balarabe Surajo, yayin.
Da yake jawabi a lokacin ziyarar, shugaban tawagar ya ce alakar da ke tsakanin Masarautar Karaye da garin Garo dadaddiya ce, tare da bayyana kwarin gwiwar masarautar kan muhimmiyar rawar da Mataimakin gwamnan wajen ci gaban Kano a sabon mukaminsa.
A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan Alhaji Murtala Sule Garo yabawa ziyarar tawagar, inda ya bayyana Sarkin Karaye a matsayin jagora mai daraja wanda shawarwari da addu’o’insa ke da matukar amfani.
Wakilin mu Kamal Umar Kurna ya rawaito mataimakin gwamnan Alhaji Murtala Sule Garo na addu’ar Allah ya karbi aikin Hajjin Sarkin na Karaye da sauran alhazan Najeriya da fatan dawowar su gida lafiya bayan kammala aikin Hajjin.
