Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar dokokin Kano ta amince da dokar kula da mata masu juna...

Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kula da mata masu juna biyu da kananan yara kyauta a asibitoci

Date:

Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar kula da mata masu juna biyu da kananan yara kyauta a asibitocin jihar Kano.

Wannan ya biyo bayan tsallake karatu na uku da dokar tayi yayin zaman majalisar a Larabar nan karkashin shugaban ta Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari.

Dokar dai zata bada damar kulawa da mata masu juna biyu da jarirai kyauta a asibitocin jihar Kano.

A dai zaman, majalisar ta amince da karatu na biyu na kudirin dokar hukumar samar da tituna a karkara ta jihar Kano.

Da yake jawabi a zauren majalisar shugaban masu rinjaye Labaran Abdul Madari, ya ce samar da hukumar zai taimaka wajen gina hanyoyi da tituna a karkara domin cigaban su.

Ya ce hukumar samar da titunan zata taimaka wajen bunkasa harkokin noma da kasuwanci a karkara da kuma ingantuwar tsaro.

Majalisar ta amince da karatu na biyu na gyaran dokar hukumar taimakekeniya a harkar lafiya ta jihar Kano.

Latest stories

Related stories