Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci birnin Landan domin halartar bikin nadin sabon Sarkin Ingila Charles lll.
Mataimaki namusamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Adesina ya ce Buhari zai bar kasar a wannan Laraba 3 ga watan Mayu, don halartar bikin nadin Sarki Charles lll.
Ana dai shirin gudanar da bikin nadin ne ranar Asabar 6 ga watan Mayu a fadar sarkin da ke Birtaniya
Shugaba Buhari zai samu rakiyar sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha, da ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, da kuma ministan yada labarai na kasa Lai Mohammed.
