Saurari premier Radio
41.7 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamna Ganduje zai karbo makudan kudin haraji daga gwamnatin tarayya

Gwamna Ganduje zai karbo makudan kudin haraji daga gwamnatin tarayya

Date:

Gwamna Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci majalisar dokokin Kano data sahalewa gwamnati Kano karbo kudin haraji na Stamp Duties daga gwamnatin tarayya.

Tun da fari dai kungiyar gwamnonin kasar nan ne suka nemi gwamnatin tarayya data basu kudin nasu wanda ta rike tun daga shekarar 2015 zuwa 2022.

Gwamnatin tarayya ta amince zata baiwa gwamnoni kudin amma da sharadin sai sun nemi sahalewa daga majalisun dokokin jihohin su wanda hakan yasa gwamna Ganduje ya rubuta takarda yana neman majalisar dokokin Kano data amince masa ya karbo wadannan kudi.

Da yake jawabi a zauren majalisar shugaban masu rinjaye Labaran Abdul Madari, ya ce kudin kashi uku ne kuma idan majalisar ta amince za a baiwa gwamnati kaso daya a yanzu yayin da za a bayar da ragowar a watanni masu zuwa.

Ya ce idan an karbo kudin za ayiwa al’ummar jihar Kano da kananan hukumomi ayyuka dasu.

Tuni dai Majalisar karkashin kakakinta Hamisu Ibrahim Chidari, ta amince da bukatar gwamnan na karbo wadannan kudi.

Latest stories

Related stories