Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiEFCC za ta kwace gidaje sama da dari uku da aka gina...

EFCC za ta kwace gidaje sama da dari uku da aka gina su da kudaden haramun a jihar Kano.

Date:

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa ta’annati ta EFCC, ta ce wata kotu ta ba ta damar karbe gidaje 324 a nan Kano, wadanda ake zargi an gina su ta hanyar amfani da kudaden haramun.

Da yake magana bayan yanke hukuncin a Larabar nan, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce galibin kadarorin na nan a wasu yankuna masu tsada da ke jihar nan.

Ya ce Mai Shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya bayar da umarni a karbe gidajen kamar yadda EFCC ta bukata.

Hukumar ta ce gidajen sun hada da guda 168 da ke Sheikh Ja’afar Mahmud Adam wato Bandirawo City da guda 122 da ke Sheikh Nasiru Kabara wato Amana City da kuma 38 da ke Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu City.

EFCC ta kara da cewa gidajen sun hada da masu dakuna biyar-biyar, hurhudu, uku-uku da masu biyu-biyu da sauransu.

A cewarta, ana zargin an gina gidajen ne da kudin da aka samu ta hanyar haramun daga hukumar kula da yan fansho ta jihar Kano.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...