Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn nada sabon sarki Charles III sarautar Ingila

An nada sabon sarki Charles III sarautar Ingila

Date:

An nada yarima Charles III sarautar sarkin Ingila.

Wannan shine karo na farko a tarihin Burtaniya cikin shekaru 70 da aka nada sabon sarki tun shekarar 1953.

Da misalin karfe 12:02 na yau asabar, Archbishop na Canterbury Justin Welby ya sanya kambin zinari na St Edward a kan Charles III wanda shine ke tabbatar da shi a matsayin Sarkin Burtaniya, kuma magaji ga sarauniyar Elizabeth data rasu a shekarar 2022.

Kambun zinaren da aka saka wa Sarki Charles III a yau domin naɗin sarautarsa a matsayin sarkin Ingila ya kai shekara 360 da ƙirƙiri kuma shine basarake na bakwai da ya saka shi a tarihin Burtaniya.

Latest stories

Related stories