Saurari premier Radio
34.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAn rantsar da mace ta farko a matsayin babbar mai sharia’a a...

An rantsar da mace ta farko a matsayin babbar mai sharia’a a jihar Adamawa

Date:

 

Gwamnan jihar Adamawa Ahamadu Umaru Fintiri, ya rantsar da mace ta farko  Hafsat AbdulRahman, a matsayin babbar Mai Shari’a kuma alkaliyar-alkalan jihar, ranar Litinin, a gidan gwamnati dake Yola fadar jihar Adamawa.

Haka kuma cikin mutanen da gwamnan ya rantsar sun hada da Ibrahim Sudi da Audu Balami, a matsayin manyan alkalan kotun Shari’ar Musulunci da kotun daukaka kara ta shari’ar gargajiya.

Da yake jawabi jim kadan da rantsarwar gwamna Ahamadu Umaru Fintiri, yace sabbin alkalan-alkalan jihar su na da cikakken ikon gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta ba su, saboda haka zaiyi aiki da su a matsayinsu na cikakkun alkalai.

Gwamnan ya kuma yabawa babbar Mai shari’a Hafsat AbdulRahman bisa kwarewa da gogewa da jajircewar da take dashi, da yace hakan ya kai ga kwarewarta da rike mukamai a fannin shari’a a tsawon shekarun aikin da ta yi.

 

Latest stories

Related stories