Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMajalisa Ta Yi Sammacin Tsohon Ministan Jiragen Sama Hadi Sirika Kan Batun...

Majalisa Ta Yi Sammacin Tsohon Ministan Jiragen Sama Hadi Sirika Kan Batun Jirgin Nigeria Air

Date:

Majalisar wakilai ta yi sammacin tsohon ministan jiragen sama Hadi Sirika kan inda aka kwana a batun jirgin Nigeria Air da tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari ta kaddamar.

An dai ta sukar tsohon ministan bayan da kamfanin jirgin sama na Ethiopia Airline ya barranata kansa da batun kafa sabon kamfanin na Nigeria Air, kuma ya karbe jirgin sa guda daya da aka kaddamar.

Majalisar wakilan ta yi sammacin Hadi Sirika, domin yayi mata bayani kan inda aka kwana a batun kafa kamfanin jirgin Nigeria Air da aka sha takaddama akai.

Gayyatar tsohon ministan ta biyo bayan amincewa da kudurin da dan majalisa, Tarkighie Dickson ya gabatar, inda ya ce a 2016 tsohon ministan ya kaddamar da sabon jirgin Nigeria Air da alkawarin kammala aikinsa kafin karewar tsohuwar gwamnatin Muhammadu Buhari.

Kuma bayan wannan ne aka nunawa al’ummar kasa wani jirgi da aka ce an karbo hayar sa ne daga kamfanin Ethiopian Airline kuma aka yi masa fenti, amma daga bisani sai kamfanin ya karbe abinsa.

Dan majalisar ya kara da cewa gwamnatin baya ta narka biliyoyin Naira kan batun amma ba’a samu wani kwakkwaran bayani ba.
Batun jirgin Nigeria Air, ya janyo cece-kuce tsakanin yan Najeriya musamman bayan kamfanin jirgin Ethiopia ya musanta shiga wata yarjejeniya da ma’aikatar sufurin jiragen saman kasar nan.

Majalisar dai ta amince da bukatar bayyanar tsohon minisitan da kuma hukumar kula da zirga-zirga jiragen sama a gabanta.

Wani bincike da premier radio ta yi a baya ya tabbatar da cewa jirgin na kasar Ethiopia mai lamba ET APL tuni ya koma cikin yan uwansa tare da ci gaba da zirga zirga kamar da.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...