Saurari premier Radio
31.2 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoMajalisar Wakilai Ta Bukaci Hukumar Sadarwa NCC Ta Tabbatar Layukan Sadarwa Sun...

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Hukumar Sadarwa NCC Ta Tabbatar Layukan Sadarwa Sun Daina Daukarwa Al’umma Kudin Na Babu Gaira Babu Dalili

Date:

Majalisar wakilai ta bukaci hukumar sadarwa NCC ta tabbatar layukan sadarwa sun daina daukarwa al’umma kudin kira na babu gaira babu dalili.

Majalisar ta ce akwai matsalolin da masu amfani da layukan sadarwa ke fuskanta ta bangaren kira da kuma aikewa da sakonni.

Da yake gabatar da bukatar a zauren majalisar, Emmanuel Ukpong daga jihar Edo, ya ce akwai akalla yan Najeriya sama da miliyan 222 da suke amfani da layukan sadarwa kamar yadda hukumar kididdiga ta kasa NBS ta fitar a rahotonta na 2022.

A tsokacinsa kan hakan, kwararre kan na’ura mai kwakwalwa, Sani Ado Maikwalla, a zantawarsa da wakilinmu Faisal Abdullahi Bila, ya ce matsalar da ake fuskanta ta bangaren kiran waya a wasu lokutan ba laifin hukumar sadarwa bane sai dai kamafanin layukan.

A yan kwanakin nan dai masu amfani da wayoyin hannu na yawan korafi kan matsalar da suke fuskanta ta yawan daukar na babu gaira babu dalili a lokacin kiran waya ko kuma yayin aikewa da sakonni.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...