Saurari premier Radio
41.6 C
Kano
Wednesday, May 1, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoNational Para Games 2023:Gwamnatin Kano ta kasa cika mana alkawarin da ta...

National Para Games 2023:Gwamnatin Kano ta kasa cika mana alkawarin da ta dauka-Yan Wasan Para Games

Date:

Gwamnatin Kano ta gaza cika alkawarin biyan tawagar da suka wakilci Kano, a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta masu bukata tamusamman ta kasa da aka kammala a birnin tarayya Abuja.

Da fari gwamnatin Kano ta bakin mai rikon shugabancin hukumar Wasanni ta jihar Kano, Malam Bala Sani ya ayyana ranar Larabar data gabata a matsayin ranar da gwamnatin za ta kammala biyan kudaden na Alawus din tawagar.

Malam Bala wanda ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai a ranar da tawagar Kano ke shirin baro Abuja zuwa Kano bayan karkare gasar.

Malam Bala ya ce tuni gwamnatin ta kammala shirin biyan kudaden na yan wasan tawagar, da jami’an Lafiya da yan Jaridun da suka je domin kawo labarin yadda aka yi gasar.

To sai dai zuwa wannan Larabar da ke kasancewa ranar da gwamnatin ta Kano ta ayyana, domin biyan kudaden rahotanni sunce babu wani labari na biyan kudaden.

Haka zalika an jiyo shima kwamishinin Raya Karkara wanda ke zama kwamishinan dake lura da harkokin wasanni ya ce gwamnatin Kano zata biyan kudin zuwa Larabar nan.

Safiyanu Hamza Kachako ya tabbatar da hakan ne a wani taron manema labarai da ya jagoranta a ofishin hukumar wasanni a ranar Talata, inda ya bayar da tabbacin cewa za a biya kudin.

Kachako Ya ce dama matsalar samun sauyin sabon sakataren gwamnatin Kano ne ya kawo jinkirin sakin kudaden na tawagar da ta wakilci Kano a gasar da aka gudanar a Abuja.

Har wa yau wakilinmu Ahmad Hamisu Gwale ya sake tuntubar kwamishinan da ke lura da harkokin wasanni Safiyanu Kachako amma wayar sa bata shiga.

An jiyo ma wasu cikin Yan wasan Tawagar da suka Wakilci Kano a gasar suna kukan gwamnatin ta kasa cika musu Alkawarin biyansu kudaden Alawus-Alawus.

Guda cikin Yan wasan da ya bukaci a sakaye sunansa zantawarsa da Ahmad Hamisu Gwale ya ce har kawo yanzu babu Labarin biyansu kudaden Alawus-Alawus din da gwmanatin Kano tayi musu Alkawari.

Tawagar Jihar Kano dai a gasar Motsa Jiki ta masu bukata ta musamman ta kasa, ta samu lambobin yabo na Zinare 18 a gasar da aka buga a birnin tarayya Abuja.

Jihar Kano ta fafata a wasanni 12 cikin 15 da aka gudanar a gasar, wadda ma’aikatar matasa da wasanni ta kasa ta shirya a karo na biyu a tsakanin Jihohin Najeriya.

Yan wasa da dama daga bangarori daban-daban da suka halarci gasar ne suke nuna bajintar lashe Sarkokin Zinare, Azurfa da kuma Tagulla a gasar da aka tsara daga 8 zuwa 14 ga Disambar 2023 gasar da fafata a filin wasa na Moshood Abioloa da ke birnin tarayya Abuja.

A gefe guda ma jihar Kano ta kuma lashe Lambobin yabo na Azurfa 13, baya ga lashe Lambobin Tagulla 17 a gasar da aka fafata birnin tarayya Abuja.

Duk da wannan bajintar da tawagar Kano tayi a gasar amma gwamnatin Kano ta gaza biyansu kudaden-alawus-alawus da ya kamata a bawa wadanda su kaje gasar.

Latest stories

Netanyahu ya nanata Ć™udirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta Ć™asa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...

Related stories

Netanyahu ya nanata Ć™udirin sojojin Isra’ila na kai farmaki ta Ć™asa a Rafah.

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nanata kudirin sojojin Isra'ila...

NiMet ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama a wasu jihohin.

Wani has ashen hukumar Kula da Yanayi ta kasa...