Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoKowanne Kamfani Sai Ya Nemi Izinin Hukumar Ta Ce Fina-Finai Kafin Ya...

Kowanne Kamfani Sai Ya Nemi Izinin Hukumar Ta Ce Fina-Finai Kafin Ya Fara Daukar Film – Al-Mustapha

Date:

Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ta ce daga yanzu duk kamfanin da zai yi aikin daukar shirin film sai ya sanar da ita.

Yayin zantawarsa da Premier radio, shugaban hukumar, Abba Al-Mustapha, ya ce hakan ya biyo bayan gyare-gyaren da hukumar ta zo da shi domin tsaftace harkar film a tsakanin al’umma.

Ya ce dama wannan ba sabon abu ne, kara tabbatar da dokar aka yi ta hanyar bayar takardar sahalewar aiki.

Ya ce sun dauki matakai domin sanin ainahin masu yin aikin fina-finai da kuma bara gurbi.

Al-Mustapha ya kara da cewa takardar sahalewar za ta bai wa masu shirya fina-finan damar yin aiki a jihar Kano.

Shugaban Hukumar tace fina-finan ya yi kira ga abokan huldarsu da su ci gaba da bai wa hukumar hadin kai domin samun nasarar abin da aka sa gaba.

Latest stories

Related stories