Saurari premier Radio
36.9 C
Kano
Friday, May 3, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar Dillalan Man Fetur IPMAN, Za Ta Shiga Yajin Aiki A Farkon...

Kungiyar Dillalan Man Fetur IPMAN, Za Ta Shiga Yajin Aiki A Farkon Sabuwar Shekara.

Date:

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN, ta ce za ta sanar da matsayarta kan kudaden dakonsu da gwamnatin tarayya ta rike musu.

Sakataren kudi na kungiyar, Alhaji Musa Yahya Mai Kifi ne ya bayyana hakan a zantawarsa da wakiliyarmu, Hauwa Halliru Gwangwazo.

Mai Kifi ya ce gwamnatin tarayya ta rike wa mambobinta kudin dakonsu da ya haura Naira biliyan 15.

Ya ce saboda haka za su samar da matsaya ta rufe gidajen mansu bayan bukukuwan kirismeti da na sabuwar shekara.

Ko a ranar Alhamis ma, shugaban kungiyar ta IPMAN dake kula da jihohin Anambra, Ebonyi da Enugu, Mr Chinedu Anyaso, ya yi barazanar cewa yayan kungiyar za su tsayar da aiki idan har gwamnatin tarayya bata biyasu hakkokinsu ba.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Muna duba batun mafi karancin albashi-Gwamnoni.

Kungiyar gwamnonin kasar nan, ta ce kawo yanzu tuni...