Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYadda Wata Matar Aure Ta Yiwa Wani Matashi Kisan Gilla Ta Hanyar...

Yadda Wata Matar Aure Ta Yiwa Wani Matashi Kisan Gilla Ta Hanyar Caccaka Masa Wuka A Kahon Zuciya

Date:

Wata matar aure Hafsat Surajo, ta yiwa yaron gidanta Nafi’u Hafizu, kisan gilla ta hanyar caccaka masa wuka a kahon zuciyarsa da wasu wurare da dama a jikinsa.

Matar dai ta ce wanda ta kashe din yana da matukar muhimmaci a wurinta, hasalima shi ne wanda ke kular mata da dukkanin abubuwan da suka shafi kasuwancinta.

Da safiyar Juma’ar nan ne aka wayi gari da wannan labari mai daure kai a yankin Unguwa Uku da ke karamar Tarauni a jihar Kano, in da Hafsat Suraj, ta hallaka matashin Nafi’u Hafizu, dan asalin jihar Bauchi da ke a matsayin yaronta, ta hanyar caccaka masa wuka.

Da take karin bayani kan yadda ta aikata kisan a shalkwatar yan sandan Kano, Hafsatu ta ce ta yi yunkurin hallaka kanta ne, amma matashin ya hanata, ita kuma ta ga bari ta huce a kansa.

Ta ce ita kadai ta hallakashi ba tare da hannun kowa ba, kuma ta yi hakan ne ba a hayyacin ta ba, hasalima tana fama da cutar damuwa.

A cewarta ta yi yunkurin hallaka kanta ne shi kuma ya shigo don ya hanata, sai suka kaure da kowowa inda ta yanke da wukar a hannu, bayan ya kwace ne kuma ya ce ta shiga bandaki ta yi wanka.

Sai dai bayan fitowar ta daga bandakin ne kuma ta ganshi kwance a falonta, hakan ta sa ta lallaba ta dauki wukar ta kuma caccaka masa a kahon zuwciya da wasu sassan jikinsa.

Bayan ta aikata hakan ne kuma ta kira mijinta Dayyabu Abdullahi, ta sanar masa abinda ya faru, ita kuma ta fice ta tafi kyamis domin a dubata.

Sai dai a cewar mijin bayan ya dawo ne ya ga ta’asar da matar tasa ta aikata, nan take kuma ya nemo wani dattijo da yake aiki tare da shi domin a yi dabarar yadda za a kawar da gawar.

Da yake amsa tambayar jami’an tsaro alaramman da ya wanke gawar yayi mata sutura, ya ce shi kam taimako ya yi amma babu hannusa a cikin kisan.

Muhammad Hussaini Gumel, shi ne kwamishinan yan sandan jihar Kano ya kuma yi karin bayani kan yadda suka samu labarin kisan da ma yadda wannan mata ta aikata kisan.

A yanzu dai rundunar yan sandan na gudanar da bincike kan lamarin inda ta ce da zarar ta kammala za ta aike da wadanda ake zagi zuwa kotu domin yi musu hukunci.

Latest stories

Related stories