Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoGwamnatin Kano ta cika Alkawarin biyan Yan wasan Para Games

Gwamnatin Kano ta cika Alkawarin biyan Yan wasan Para Games

Date:

Gwamnatin Jihar Kano ta biya kudaden Alawus-Alawus din yan wasa da wasu cikin wadanda suka wakilci Jihar a gasar Masu bukata ta musamman ta kasa da a kayi a birnin Tarayya Abuja.

Mai rikon Shugabancin hukumar wasanni ta jihar Kano
Malam Bala Sani ne ya jagoranci biyan kudaden a ranar Asabar a Ofishin hukumar da ke nan Kano.

Malam Bala Sani ya ce da ma tsaiko aka samu wajen biyan kudaden Alawus-Alawus din a baya, wanda a yanzu tuni suka biya Yan wasan.

Ya kuma ce a mako mai zuwa ake saran kammala biyan kudaden Alawus-Alawus ga masu horas wa jami’an lafiya da kuma duka tawagar da su ka wakilci Kano a gasar.

Har wa yau suma dai Yan Jaridun da suka je gasar domin kawowa masu sauraro yadda take wankana, Gwamnatin ta ya ba musu da kuma saka musu bisa Kokarin da sukayi.

Malam Aminu Tudun Wada da ya yi magana a madadin yan wasan da aka biyasu kudaden ya bayyana farin cikinsu da biyansu kudaden da akai musu.

Idan ba a manta ba dai Tawagar Kano a gasar ta masu bukata ta musamman da aka kammala a Abuja ta karkare a matsayi ta Uku bayan lashe sarkokin Yabo 47 jumulla.

Gasar ta Natioal Para Games wadda ma’aikatar Matasa da Wasanni ke shiryawa ta gudana daga 8 zuwa 14 ga Disambar 2023 a filin wasa na Moshood Abioloa da ke birnin Tarayya Abuja.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...