Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Thursday, May 16, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaKungiyoyin kwadago na kasa NLC da TUC zasu tsunduma yajin aikin sai...

Kungiyoyin kwadago na kasa NLC da TUC zasu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Date:

Kungiyoyin kwadago na kasa NLC da TUC zasu tsunduma yajin aikin bai daya a fadin kasar nan ranar Talata 14 ga watan Nuwamba 2023.

Shugabannin kungiyoyin biyu sun cimma wannan matsaya ne bayan wani taron majalisar zartarwa ta kasa na musamman da aka gudanar a ranar Talatar nan a Abuja.

Matakin da kungiyar kwadagon ta dauka ya biyo bayan cin zarafin shugaban NLC na kasa, Joe Ajaero, a makon jiya a jihar Imo.

Tun a safiyar gobe laraba yan kwadago a jihar Imo zasu tsunduma yajin aiki kafin sauran yan kungiyar su biyo baya.

Kungiyar kwadagon de na zargin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo, Mohammed Barde da hannu a harin da aka kaiwa Ajaero a Owerri, babban birnin jihar Imo.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...