Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoMungaji bashin daya zarce naira miliyan dubu 500 daga Ganduje - Gwamnatin...

Mungaji bashin daya zarce naira miliyan dubu 500 daga Ganduje – Gwamnatin jihar Kano

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta ce tsohon gwamna, Abdullahi Umar Ganduje, ya bar bashin da yawansa ya zarce Naira miliyan dubu 500.

Mataimakin gwamna, kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ne ya bayyana hakan lokacin da yake jagorantar taron uwar jam’iyyar NNPP na shiyyar Arewa maso yamma a Kaduna, inda yace bashin da gwamnatin suka ga da ta bari zai zarce biliyan 500 idan gwamnatin su ta gama hada alkalumanta.

Gwarzo ya ce tarin bashin da suka gada shine ya zame musu barazanar da ya hana gwamnatinsu fara aiwatar da tsarukanta gadan gadan tun bayan data karbi mulki.

Mataimakin gwamnan sai ya bayyanawa iyayen jam’iyyar ta su wasu daga cikin irin aikace aikacen da gwamnatinsu ta fara aiwatarwa da dan abinda suka samu a lalitar gwamnatin kano, tare da tabbatar musu da cewa mulkin da suke gudanarwa a kano zai fitar da uwar jam’iyyar tasu kunya.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...