Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKotu ta tabbatar da Simon Lalong a matsayin Sanatan filato ta Kudu

Kotu ta tabbatar da Simon Lalong a matsayin Sanatan filato ta Kudu

Date:

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da Ministan Kwadago, Simon Lalong a matsayin zababben Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu.

Idan za a iya tunawa hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana Sanata Napoleon Bali na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben.

Sai dai a ranar 11 ga watan Satumba ne kotun sauraren kararrakin zabe ta kasa da na jihohi da ke zamanta a Jos ta ayyana Simon Lalong a matsayin zababben Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu, yayin da ta soke nasarar Napoleon Bali na jam’iyyar PDP sanadiyar magudin da akai a zaben fidda gwani.

Tun da fari dai jamiyyar APC ta kalubalanci yanda jamiyyar PDP ta gudanar da zaben fidda gwani daya bawa Napoleon Bali nasarar zama dan takarar kujerar sanatan

Kafin samun nasara a kotun sauraren karrakin zaben Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Lalong a matsayin ministan kwadago da samar da aikin yi.

kotun daukaka karar karkashin mai shari’a Williams Daudu ya tabbatar da hukuncin da kotun farko tayi. Inda ya ayyana Lalon a matsayin halastaccen Sanatan mai wakiltar filato ta kudu

Latest stories

Related stories