Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar dattawan Arewa ta nuna damuwa kan rashin jituwar da ke tsakanin...

Kungiyar dattawan Arewa ta nuna damuwa kan rashin jituwar da ke tsakanin manyan attajirai Dangote da BUA.

Date:

Kungiyar dattawan Arewa ta bayyana damuwa kan rashin jituwar da ke faruwa tsakanin manyan yan kasuwar yankin, Alhaji Aliko Dangote da Abdussamad Rabiu na Kamfanin BUA, in da suka yi zargin cewa wannan fada na shafar tattalin arziki da siyasar yankin.

Haka kuma kungiyar ta ce ta damu da yakin sankuru da faruwa tsakanin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle da gwamna mai ci Dauda Lawal, inda suka yi kira ga yan siyasar da su rungumi zaman lafiya.

Wata sanarwa da shugaban kungiyar, Farfesa Ango Abdullahi ya fitar, ta ce rikicin dake faruwa a yanzu, tsakanin Aliko Dangote da Abdussamad Isiyaku Rabiu kan farashin siminti da kuma rikicin kudi tsakanin gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, na kara ta’azzara kalubalen da yankin Arewa ke fuskanta a fannin tsaro da tattalin arziki.

Saboda haka ta yi kira ga shugabannin da ke da hannu a cikin rikice-rikicen da su yi taka tsantsan tare da yin kira ga dukkan shugabanni da masu ruwa da tsaki a Arewa da su shiga tsakani ta hanyar gudanar da taron sulhu a tsakanin dukkan bangarorin.

Ta ce kalubalen da Zamfara ke fuskanta na bukatar hadin kai, kuma ta hanyar hada kai ne kawai za a iya shawo kan rikice-rikicen da jihar ke fama dashi.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...