Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiCBN ya bayar da tabbacin ci gaba da amfani da tsoffin takardun...

CBN ya bayar da tabbacin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na Naira

Date:

Babban bankin kasa CBN ya gargaɗi masu ƙin karɓar tsofaffin takardun kudi na Naira a fadin kasar nan, in da ya bayar da tabbacin ci gaba da amfani da tsoffin kudaden.

Wannan na zuwa ne sakamakon fargabar da ake ciki cewa tsofaffin takardun kuɗi za su daina aiki nan da watan Disambar bana.

Wata sanarwar da mai magana da yawun CBN, Isah Abdulmunin ya fitar a Larabar nan, ta ce bankin bai bayar da umarnin janye tsofaffin takardun kudin ba daga wajen al’umma.

Bankin ya ce an kuma samu rahotannin damuwa da wasu jama’a ke nunawa kan halacci ko rashinsa na tsoffin takardun kudin Naira.

CBN ya ce akwai isassun takardun kudi a fadin kasar nan domin gudanar da duk harkokin tattalin arziki na yau da kullun, in da ya kara da cewa duk wata takardar kudi, za ta ci gaba da aiki kuma bai kamata a yi watsi da ita ba.

Babban bankin ya umarci rassansa a faɗin ƙasa da su ci gaba da bayar da tsofaffin takardun kuɗi da kuma sabbi don ci gaba da rarrabawa ga abokan hulɗar bankuna.

Latest stories

Related stories