Saurari premier Radio
27.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar mawakan Hausa sun nemi afuwar tsohon shugaban kasa Buhari kan kalaman...

Kungiyar mawakan Hausa sun nemi afuwar tsohon shugaban kasa Buhari kan kalaman Rarara

Date:

Kungiyar mawakan Hausa sun nemi afuwar tsohon shugaban kasa Buhari kan kalaman Rarara.

Kungiyar mawakan hausa da ake kira (One Voice Association) sun barranta kansu da kalaman mawaki Rarara na sukar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Cikin wani bidiyo da ya karade kafafen yada labarai sun nuna yadda Rarara ya kalubalanci gwamnatin Buhari, inda ya bayyana ta a matsayin mara nasara data haddasa wahala ga ‘yan kasa.

Saidai kuma kungiyar (One Voice Association) ta bayyana rashin amincewar ta da kalaman Rarara, mambobin kungiyar sunce Rarara yayi kalaman ne a karankansa.

Kotu ta umarci ‘yan sanda su binciki Ado Gwanja da Safara’u

Shugaban kungiyar Ali Jita, yace a matsayin su na mawaka suna girmama manya da sauran mutane da suka shugabanci kasar nan batare da la’akari da kabila ba.

Ali Jita, yace kalaman Rarara sun saba da tarbiya da dabi’un mawaka.

Yace kamar kowane mutum shugaba Buhari yana da matsalolin sa amma duk da yayi iya nasa kokarin a kasar nan.

Mataimakin kungiyar Ado Isah Gwanja ya bayyana shirin su na ziyartar tsohon shugaban kasa Buhari a Daura domin neman afuwar sa kan kalaman da Rarara yayi masa.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...