Kungiyar kwadago ta TUC reshen jihar Kano, ta ce za ta binciki dalilin rashin biyan ma’aikata dubu 20-20 da gwamnatin jihar ta yi alkawarin farawa daga watan Disambar bara.
A shekarar da ta gabata ne gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi alkawarin yiwa ma’aikatan kananan hukumomi da na jiha karin dubu 20n-20n a albashinsu na tsawon wata shida, wanda zai fara daga watan Disambar 2023, da nufin rage musu radadin rayuwa.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa tuni aka fara biyan albashin watan Janairu ba tare da karin dubu 20-20 din ba.
Shugaban kungiyar kwadagon ta TUC reshen Kano, kwamred Mubarak Buba Yarima, ya shaidawa wakiliyarmu, Hauwa Halliru Gwangwazo, cewa za su tuntubi gwamnatin Kano kan wannan batu, sai dai ya ce ma’aikatan su sani cewa kudin zai zo ne daban ba wai a cikin albashinsu ba.
Gwamnatin Kano dai ta yi alkawarin inganta rayuwar ma’aikatan jihar domin samun ci gaba.