Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKasuwar Musayar Kudaden Waje Ta Kano Ta Rage Lokacin Aiki, Bayan Rufe...

Kasuwar Musayar Kudaden Waje Ta Kano Ta Rage Lokacin Aiki, Bayan Rufe Ta Abuja Saboda Tashin Dalar Amurka

Date:

Kungiyar yan kasuwar sauyin kudi da ke Abuja, ta ce daga yau Alhamis za ta rufe kasuwar har sai abin da hali ya yi, sakamakon tsadar dala da ke ake fama da ita a kasar nan.

Da yake sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja, shugaban kungiyar, Alhaji Abdullahi Dauran, ya alakanta tashin farashin Dalar da ayyukan kamfanin hada-hadar kudaden Intanet na Crypto da ake kira Binance.

Wanda ya ce hakan ne ya sa kungiyar yin kira ga gwamnatin tarayya, ta hana yan kasar nan hulda da kamfanin na Binance, idan har ana son karyewar Dalar.
A jihar Kano ma yan kasuwar hada-hadar kudaden ketaren ta Wapa, sun bi sahun takwarorinsu na Abuja, in da a yau din suka raje awanninsu na aiki.

Sun dauki matakin ne da nufin dakile tashin da Dalar Amurkan ke yi a kan Naira.

A cewar shugaban kasuwa, Sani Salisu Dada, hakan zai yi tasirin wajen rage karyewar darajar Naira.

To sai dai wasu rahotanni sun ce hukumar tsaron farin kaya DSS da hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC sun soma bincike domin gano dalilin tashin Dala a kasuwar musayar kudin.

Kafar yada labarai ta TRT ce ta rawaito sakataren kasuwar sauyin kudi ta WAPA a nan Kano, Haruna Musa Halo, na cewa sun rufe kasuwar ne sakamakon kiraye-kirayen da DSS da EFCC suke yi musu.

To sai dai shugaban kasuwar ta WAPA, Sani Salisu Dada, ya musanta wannan ikirari.

Wannan dai na zuwa ne, yayin da darajar Naira ta yi faduwar da ba ta taba yi ba cikin gomman shekaru na tarihi.

Inda a Talatar da ta gabata, aka musanya Dala a kan Naira 1,520 yayin da a hukumance ake sayar da Dala kan Naira 892 da N910.

A wanj bangaren kuma majalisar dattawa, ta gayyaci gwamnan babban bankin kasa CBN, Mista Olayemi Cardoso, da ya bayyana a gabanta domin yin bayani kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki da kuma faduwar darajar Naira a kasuwar musayar kudaden waje.

A jiya Laraba ne majalisar ta hannun kwamitinta mai kula da harkokin bankuna da inshora da sauran cibiyoyin kudi, ta gayyaci Cardoso, da ya bayyana a gabanta ranar Talata mai zuwa domin bayar da bahasi kan matsalolin da ke neman gurgunta tattalin arzikin kasa.

Kwamitin karkashin shugabancin Sanata Adetokunbo Abiru, ya gana ne bayan da a jiyan, inda suka mika gayyatar ga gwamnan na CBN domin ya je ya yi bayani kan mafita.

Da yake magana da manema labarai bayan taron nasu na sirri, Sanata Abiru, ya ce halin da tattalin arzikin kasar nan ke ciki musamman hauhawar farashin kayayyaki abu ne da ya damu yan majalisar.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...