Saurari premier Radio
25.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKotu Ta Bayar Da Umarnin Rufe Asusun Bankunan Hukumar Hisbah ta jihar...

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Rufe Asusun Bankunan Hukumar Hisbah ta jihar Kano Bayan Wasu Masu otal Suka Gurfanar Da Ita

Date:

Wata kotu a nan Kano, ta bayar da umarnin rufe asusun bankuna na hukumar Hisba ta jiha, biyo bayan gurfanar da ita da wasu masu otel-otel suka yi a gaban kotun.

Da yake tabbatar da hakan a wata tattaunawa da TRT Afrika, Babban kwamandar hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce sai dai har kawo yanzu ba a sanar da su laifin da suka aikata ba da ya kai ga rufe asusun nasu.

Daurawa ya ce an dai aika musu takardar kotu cewa akwai wani otal da suka taba zuwa aiki, wanda suka ce sai sun biya su Naira 700,000, sai kuma wani daban da shi ma suka taba zuwa, shi ma za su biya Naira 100,000.

Ya ce daga nan suka ce dole sai sun biya Naira 800,000 shi ne sai aka rufe asusun nasu.

Kwamandan na Hisba, ya ce ya kamata a gaya musu laifin da suka yi domin su nemi lauya ya shiga cikin zancen, idan sun kasa kare kansu sai a yi musu hukunci.

Sai dai ya ce ya tura wakili ya je ya samu babban lauyan jihar Kano, domin ba a gaya musu laifinsu ba da kuma dalilin hakan.

Daurawa ya koka cewa wannan abu da aka yi musu ya dakatar da duka ayyukansu tunda ba za su iya taba kudaden cikin asusunsu ba.

A kwanakin baya ne dai, hukumar ta Hisbah ta rika samame kai wasu otel-otel da wuraren shakatawa a nan Kano, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce.

Latest stories

Related stories