Saurari premier Radio
41.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasar Ukraine ta tallafawa Najeriya da hatsi tan 25,000

Kasar Ukraine ta tallafawa Najeriya da hatsi tan 25,000

Date:

Gwamnatin Ukraine ta bayyana shirinta na samar da cibiyoyin hatsi a Najeriya da sauran kasashen Afirka yayin da ta ba Najeriya gudummawar kimanin tan 25,000 na hatsi domin bunkasa alakar kasashen biyu.

Ministan abinci na Ukraine, Mykola Solskyi, ne ya bayyana haka a ranar Talata, a Abuja, yayin ganawa da ministan harkokin waje na kasar nan Geoffrey Onyeama.

Solskyi, ya ce hatsin zai iso Najeriya daga Ukraine a watan Fabrairu karkashin shirin kasar da ake kira “Hatsi daga Ukraine”.

Ya ce duk da yakin da kasar keyi da Rasha, ma’aikatar abincin kasar na son kulla dangantaka da Najeriya, inda kuma ya godewa kasar nan bisa shirin ta na kyautata alakar kasashen biyu.

“Irin wannan ci gaba na samar da wadannan cibiyoyi zai taimaka wajen shigo da hatsi mai kyau kasar nan kuma hakan zai yi tasiri kan farashin kayan masarufi.

“Ukraine zata samar da cibiyoyin hatsi biyu zuwa uku a nahiyar afurka na kasar nan shine mafi muhimmanci kuma idan muka aiwatar dashi yadda yakamata zai zama wani mataki na daga alakar mu ta kasuwanci zuwa mataki na gaba,” a cewar Solskyi.

Da yake jawabi ministan harkokin waje na kasar nan Geoffrey Onyeama, ya jajantawa Ukraine kan yakin da takeyi da Rasha, tare da  godewa kasar bisa gudunmawar hatsin da ta baiwa kasar nan.

Onyeama, ya ce Najeriya tana da kyakkyawar alaka da Ukraine, yana mai cewa da yawan wadanda yakin Ukraine ya shafa daliban kasar nan ne kuma yakin ya haddasa tsaiko a karatun su.

A nasa bangaren ministan noma da raya karkara, Muhammad Abubakar, ya ce kasar nan zata samar da rumbunan adana hatsin a cibiyoyin da kasar ta Ukraine zata samar.

Abubakar, ya ce kaso talatin na kasuwancin da ya shafi noma kasar nan tana yine da Ukraine musamman a bangaren Alkama da Taki da sauran kayan hatsi, inda ya ce hakan zai kara karfin alakar dake tsakanin su.

Muhammad Abubakar, ya kuma ce za ayi amfani da cibiyoyin hatsin a lokutan da ake bukatar taimakon gaggawa, tare da bada tallafi ga sauran kasashen duniya.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...