Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiIyayen Yaran Da Aka Sace A Jihar Kano, Sun Bukaci A Kafa...

Iyayen Yaran Da Aka Sace A Jihar Kano, Sun Bukaci A Kafa Hukumar Dawo Musu Da Yayan Nasu

Date:

Kungiyar iyayen yaran da aka sace a jihar Kano, ta bukaci gwamnati ta kafa hukumar bincikowa da dawo da yaransu da aka sace aka kai su sassa daban-daban na Najeriya.

Shugaban kungiyar, Kwamared Isma’il Ibrahim Muhammad, ya yi kiran ta cikin zauren na Premier.

Ya ce sama da yara dari 600 ne aka sace a baya-bayan nan, kuma dole sai hukumomi sun shigo ciki domin taimakawa wajen dawo da yaran hannun iyayensu.

Wasu iyaye da aka sacewa yara kuma suka gano su a jihar Anambra sun roki gwamnatin Kano da sauran manyan Arewa, su sanya hannu wajen kwato musu yaransu da aka gano a wasu jhohi.

Zuwa yanzu, yara 18 ne kungiyar iyayen yaran da wasu iyayensu suka gani da idanunsu a gidajen raino a jihar Anambra.

Sai dai sun shaidawa Premier radio cewa, biyo bayan wani umarnin kotu, ma’aikatar mata ta jihar ta kwashe yaran daga inda suka gansu tun da farko, tare da mayar da wasunsu gidan rainon wadda ake zargi da sace yaran tun da fari.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...