Saurari premier Radio
32.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiWata Bakwai Gwamnatin Kano Ba Ta Biya Wasu Ma’aikatan Hukumar Hisbah Alawus...

Wata Bakwai Gwamnatin Kano Ba Ta Biya Wasu Ma’aikatan Hukumar Hisbah Alawus Dinsu Ba

Date:

Wasu ma’aikatan hukumar Hisba ta jihar Kano, suka koka kan kin biyansu alawus-alawus dinsu na tsawon watanni bakwai.

Ma’aiktan Hisbar da ke aiki a kananan hukumomin Kano 44, sun ce tun bayan zuwan sabuwar gwamnatin Kano aka dakatar da su saboda tan-tance su da gwamnatin ta ce za ta yi.

Sai dai har kawo wannan lokaci ba a kira su ba domin sanin a halin da suke, kamar yadda suka shaidawa Premier Radio.

Kan koken nasu, wakilinmu, Ahmad Adamu Rimin-Gado, ya tuntubi kakakin hukumar Hisbar, wanda ya ce suna sane da wannan al’amari.

Sai dai ya ce mu bashi lokaci domin ya tattauna da bangaren gudanarwar hukumar ta Hisba domin yi mana karin bayani kanda halin da ake ciki.

Latest stories

Related stories