Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAFCON: Alhassan Yusuf ya maye gurbin Ndidi a Super Eagles

AFCON: Alhassan Yusuf ya maye gurbin Ndidi a Super Eagles

Date:

Ahmad Hamisu Gwale

Dan wasan tsakiya na kungiyar kwallon kafa ta Royal Antwerp Alhassan Yusuf, ya shiga jerin yan wasan da zasu bugawa Super Eagles wasa a gasar kafin nahiyar Afrika ta AFCON a kasar Cote d’Ivoire.

Alhassan Yusuf dan asalin jihar Kano, ya shiga jerin ne bayan maye gurbin Wilfred Ndidi wanda ya ji rauni kuma ya fice a wanda zasu buga gasar ta AFCON.

Tun a ranar Litinin din data gabata Leicester City ta fafata da Huddersfield a gasar Championship, kuma Ndidi bai samu damar buga wasan ba sakamakon rauni.

Idan za a iya tunawa Ndidi bai wakilci Najeriya a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya da Super Eagles tayi da Zimbabwe ba, da hakan ke zama karo na farko cikin shekaru biyar da Ndidi bai wakilci Najeriya ba.

Tuni hukumar Kwallon kafa ta kasa NFF ta tabbatar da Yusuf a matsayin wanda zai maye gurbin Wilfred Ndidi a tawagar ta Super Eagles.

Ana sa ran a wannan Larabar Kasashe 24 da zasu buga gasar ta
AFCON, zasu mika jerin sunayen karshe na yan wasan nasu ga hukumar Kwallon kafa ta nahiyar Afrika wato CAF.

Sai dai har zuwa ranar 10 ga Janairun da muke ciki, akwai damar sauya duk dan wasan da ya ji rauni gabannin fara gasar ta wannan Shekarar a kasar Ivory Coast.

Tuni mai horar da tawagar Super Eagles Coach Jose Peseiro da wasu cikin masu ruwa da tsaki a Najeriya suka tuntubi suka sanarwa CAF cewa Yusuf zai maye gurbin Wilfred Ndidi.

Alhasssan Yusuf ya taka rawar gani a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai Champions League a kungiyar sa ta Royal Antwerp dake kasar Belgium.

Dan asalin jihar Kano Yusuf, a karon farko zai shiga sansanin Super Eagles domin bugawa tawagar wasa.

Idan za a iya tunawa Peseiro ya sanya sunan Yusuf a jerin kwarya-kwaryar yan wasa 40 da zai zaba domin bugawa Najeriya wasa a gasar ta AFCON da tuni yanzu haka ya shiga cikin jerin.

Mai shekara 22 dan asalin jihar Kano, Alhassan Yusuf ya taka rawar gani a wasan da kungiyar sa ta Antewarp ta doke Barcelona daci 3-2 a UEFA Champions League a kakar da muke ciki.

Yusuf ya taimaka an zura kwallo a wasan da akalla ya yi nisan Kilomita 13 daga wajen yadi na 18.

Alhassan Yusuf ya fara komawa IFK Göteborg a Yulin 2021, kafin ya fara bugawa Allsvenskan a shekarar 2019 wanda a daidai wannan lokacin yana bugawa Royal Antwerp, Kuma kwantaraginsa da kungiyar zai kare ne zuwa 30 ga Yunin 2025.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...