Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Tarayya Za Ta Sanya Jami’oin kasashen Niger, Uganda da Kenya Cikin...

Gwamnatin Tarayya Za Ta Sanya Jami’oin kasashen Niger, Uganda da Kenya Cikin Wadanda Za Ta Daina Tantance Karatunsu na Digirinsu

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce za ta sanya karatun digirin jami’oin kasahen Uganda, Kenya, Niger da wasu kasashen, cikin wadanda za ta dakatar da tantance su.

Wannan ya biyo bayan dakatar da na kasashen Benin da Togo da gwamnatin ta yi.

A wata hira da gidan talabijin na Channels, ministan ilimi Tahir Mamman, ya ce za su fadada yawan jami’ioin kasashen da su dakatar da tantance karatunsu na digiri, bayan na kasashen Benin da Togo da aka dakatar.

Ministan ilimin dai ya ce daliban da ke zuwa irin wadancan makarantu suna sane da matsalar saboda haka baya tausaya musu, inda ya kira su da masu laifin da ya kamata a kama.

Haka kuma gwamnatin tarayya ta haramtawa wasu jami’o’in ketare 18 tafiyar da harkokinsu a kasar nan tana mai bayyana su a matsayin masana’antun hada digiri.

Da take bayyana matakin dakatarwar cikin wata sanarwa, hukumar kula da jami’o’i ta kasa NUC, ta yi bayani cewa jami’o’in 18 ba su da sahalewar gwamnati don tafiyar da harkokinsu saboda haka ta rufe su.

Jami’oin da dakatarwar da shafa, sun hada da:

1. University of Applied Sciences and Management, Port Novo ta Jamhuriyyar Benin.
2. Volta University College, Ho, Volta Region, Ghana.
3. The International University, Missouri, USA da ke da cibiyoyi a Kano da Legas.
4. Collumbus University, UK.
5. Tiu International University, UK.
6. Pebbles University, UK.
7. London External Studies UK.
8. Pilgrims University.
9. West African Christian University.
10. EC-Council University, USA, da ke da cibiya a Ikejan Jihar Legas.
11. Concept College/Universities (London) da ke Ilorin.
12. Houdegbe North American University.
13. Irish University Business School London.
14. University of Education, Winneba, Ghana.
15. Cape Coast University, Ghana.
16. African University Cooperative Development da ke Kwatano a Jamhuriyyar Benin.
17. Pacific Western University, Denver, Colorado da ke da cibiya a Owerri.
18. Evangel University of America and Chudick Management Academic da ke Legas.

Wannan dai ya biyo bayan wani rahoton binciken kwakwaf da waikilin Jaridar Daily Nigerian ya yi, inda ya yi bad-da-kama ya samu takardar shaidar digiri daga wata jami’a a jamhuriyar Benin a cikin mako shida kacal har ya shiga cikin masu shirin hidimtawa kasa na NYSC.

A tsokacinsa kan wannan, shugaban tsangayar ilimi ta jami’ar Bayero, Dr. Ali Idris, ya ce kamata ya yi gwamnatin ta dauki kwakkwaran mataki, bama iya ga jami’o’in kasashen waje kawai ba har ma da na nan cikin gida.

Dr. Idris ya yi kira ga iyayen dake tura yayensu jami’oin kasasahen waje da su kira tantance ingancin jami’a gabanin fitar da su.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...