Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Friday, June 14, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumar Tace Fina-Finai Ta Jihar Kano Ta Fara Shirin Daukar Matakin Doka...

Hukumar Tace Fina-Finai Ta Jihar Kano Ta Fara Shirin Daukar Matakin Doka Kan Masu Reye-Raye A Tikto, Facebook Da Youtube.

Date:

Hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, ta magantu kan korafin da al’umma ke yi dangane da yadda wasu ke amfani da shafukan sada zumunta, musamman ma Tiktok da Facebook, da Youtube wajen yin abubuwan da basu dace ba.

Ta cikin shirin Zauren Premier, shugaban hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya ce nan gaba kadan hukumar za ta bullo da wata hanyar daukar matakin kan masu raye-raye da shirya bidiyon da ya sabawa al’ada da addini.

Sai dai bai yi karin bayanin kan ko hakan na nufin gyara a dokar da ta kafa hukumar ba.

“Wannan zai zama a straight warning, da duk wanda yake abusing social media musamman Tiktok, Tiktok duk wani dan jihar Kano ya kwana da shirin cewar mun kusa zuwa gunsa”

“At least akwai in da doka za ta bamu dama da zamu zo mu tsawatar, ai na ce doka ce take yi ko, to Alhamdullahi za mu bi duk process da ake bi”

Shugaban hukumar tace fina-fanan, ya kuma ce da yawa daga cikin irin wadannan shakiyyai ba ‘ya’yan kungiyar masu shirya fina-finai ba ne, amma ya tabbatar da cewa ba za a bar irin wannan ya ci gaba ba.

An dai jima ana kokawa game da yadda matasa ke amfani da shafukan sada zumunta suna yada abubuwa da suka sabawa addini da al’ada da hakan ya sa mutane da dama a jihar Kano da ma Arewa ke ta kira ga hukumomin da abun ya shafa su dauki kwakkwaran mataki a kan matsalar.

Latest stories

Related stories