Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, May 8, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan daki da...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan daki da sauran kayan daurin auren ma’aurata dubu daya da dari takwas a karkashin shirinta na daurin aure.

Date:

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta sayo kayan daki da sauran kayan daurin auren ma’aurata dubu daya da dari takwas a karkashin shirinta na daurin aure.
Babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Daurawa ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke duba wasu daga cikin kayayyakin dakin a Larabar nan.
Ya ce gwamnati ta ware Naira miliyan dari takwas domin sayan kayan sawa da kayan abinci da kayan daki da sauran kayan bukatu na bikin aure.
Ya ce kowace amarya za ta karbi katifa da matashin kai da kuma Naira dubu 20 domin fara sana’a, yayin da wasu masu hannu da shuni suka yi alkawarin bayar da gudummawa domin ganin an samu nasarar auren.
Ya kara da cewa an gindaya sharudda na zabar wadanda za su ci gajiyar shirin kuma wadanda suka saki matansu ba tare da wani uzuri ba bayan auren to gwamnati za ta tilasta, su biya abinda aka kashe musu.
Kawo yanzu dai ba a saka ranar daurin auren ba.

Latest stories

Mamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya...

Related stories

Mamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya...