Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin jihar Kano ta tsohuwar gwamnatin da bar mata gadon matsaloli masu...

Gwamnatin jihar Kano ta tsohuwar gwamnatin da bar mata gadon matsaloli masu tarin yawa a bangaren ilimi.

Date:

Gwamnatin jihar Kano ta tsohuwar gwamnatin da bar mata gadon matsaloli masu tarin yawa a bangaren ilimi.
A cewarta a yanzu haka akwai makarantun firamare 400 da suke da malamai dai-dai a shiyyar arewacin jihar, baya ga rashin tebura da kujerun zama na dalibai da dai sauran matsaloli.
Sai dai tsohuwar gwamnatin jihar ta Kano, ta ce hangen dala sabuwar gwamnatin jihar ta yi wa lamarin, domin kuwa batun wadannan matsalolin ba wai wani abu ba ne a lullube.
kwamishinan ilimi na jihar Kanon, Umar Haruna Dogowa ne yayi wannan zargin. Yace bayan kaddamar da bincike sun gano a kananan hukumomi 13 ne ake fuskanatar matsalar karancin malamai da lallaacewar gine-gine a akalla makarantu 400 dake yankin.
kwamishinan ilimin na jihar Kano, ya bayar da tabbacin sun dauki matakan warware wadannan matsalolin da ya ce sun tarar ta hanyar daukar sabbin malamai da kuma chanjawa wasu ma’aikatan gwamnatin guraben aikin zuwa makarantu.
Sai dai kuma Sanusi Sa’idu Kiru, tsohon kwamishinan ilimi a zamanin tsohuwar gwamnatin ya ce sun yi iya bakin kokari, wajen shawo kan dimbin matsalolin da ke cunkushe a bangaren na ilimi.
Yace a zamanin sa sun dauki malaman makarantar sama da dubu goma da dari takwas, hadi da zartar da dokar da ta yi tanadi a kan yadda za a rike makarantu tare da tabbatar da cewa ana samar mu su da inganttatun kayan aiki.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...