Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin Katsina zata bada tallafin ga wadanda harin ta'addanci ya rutsa da...

Gwamnatin Katsina zata bada tallafin ga wadanda harin ta’addanci ya rutsa da su

Date:

Hafsat Iliyasu Dambo

 

Gwamnatin jihar Katsina ta amince da biyan sama da Naira biliyan 2 ga mutane 13,315 da rikicin ‘yan bindiga ya rutsa da su a fadin jihar Katsina. 

 

Amincewar ta biyo bayan kwamitin da Gwamnatin ta kafa don zakulo da tantance mutanen tun daga shekarar 2020 ya gabatar da rahoton shi.

 

Mai baiwa gwamna Aminu Bello Masari shawara na musamman kan ilimi mai zurfi, Bashir Usman Ruwan Godiya, wanda ya bayyana wa manema labarai sakamakon taron majalisar zartarwa na jiha karo na biyar.

 

Ya ce za’a yi amfani da kudaden ne wajen samar da kayan abinci da kayan makaranta da kayan sawa da ilimi da kuma biyan wasu bukatu na mata da marayu da aka kashe iyayen su.

 

Ya ce tuni gwamnati ta sake kafa wani kwamiti domin aiwatar da shawarwarin.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...